Wata kotu a kasar Kongo ta yanke wa wasu sojoji biyu masu mukamin Kanar tare da wasu mutane hudu hukuncin kisa.
Wata kotun soji ce ta yanke wa mutanen hukuncin sakamakon samun su da laifin kisan wasu ’yan Chaina biyu masu hakar ma’adinai da suka yi a watan Maris.
- ’Yan bindiga sun hallaka mutum 40 a sansanin ’yan gudun hijirar kasar Kongo
- ’Yan ta’adda sun kashe masu neman mafaka a Dimokuradiyyar Kongo
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba a garin Ituri da ke kasar.
Kanar-kanar din an same su da laifin kai hari ga wata kwambar motoci da niyyar satar wasu sandunan zinare, da kuma kudi Dala 6,000 da ’yan Chainan ke dauke da su, a kan hanyarsu ta dawowa daga wurin hakar ma’adinai.
“Muna so wannan ya zama darasi ga sauran bata-garin da ke cikin rundunar sojin kasar nan” in ji Laftanar Jukes Nongo, kakakin rundunarnsojin da ke kula da yankin na Ituri mai arzikin ma’adinai.
A shekarar da ta wuce ne, gwamnatin ta Dimokuradiyya Kongo ta dora alhakin kula da harkokin yankin Ituri da na Arewacin Kivu a hannun sojoji domin su dakile yawan tashe-tashen hankula.
Sai dai hakan bai hana kai hare-hare ba.