✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke wa Evans hukuncin shekaru 52 a gidan wakafi

Kotun ta kuma yanke wa sojan da ke taimaka masa, Victor Aduba hukuncin cin sarka ta shekaru 26 a gidan kaso.

Wata Kotu ta Musamman ta yanke wa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans hukuncin daurin shekaru 52 a gidan wakafi.

Kotun wadda ke zamanta a birnin Ikeja na Jihar Legas, ta kuma yanke wa sojan da ke taimaka masa, Victor Aduba hukuncin cin sarka ta shekaru 26 a gidan kaso.

Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo ne ya yanke hukuncin, sakamakon karar da Sylvanus Ahanoni ya shigar, wanda Evans ya yi garkuwa da shi kuma ya karbi Dalar Amurka dubu 420 a matsayin kudin fansa a watan Yunin shekarar 2014.

Da yake yanke hukuncin yayin zaman kotun da aka shafe kusan awa daya, Taiwo ya ce Evans zai yi zaman gidan yarin lokaci guda kamar idan aka zartar masa da hukunci akan sauran tuhume tuhume guda 5 da yake fuskanta da suke da nasaba da laifuffukan garkuwa da mutanen.

Mai shari’a Taiwo ya ce wannan hukunci zai zama abin daukar izina ga sauran al’umma a yayin da matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta zama ruwan dare a kasar.

Ana iya tuna cewa, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sandan da aka dakatar, Abba Kyari da tawagarsa ne suka kama Evans a Legas, bayan ya kwashe dogon lokaci yana wasan buya da jami’an tsaron da suke nemansa ruwa a jallo.