✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke wa barawon Al-Kur’ani hukuncin sharar masallacin Juma’a

Kotun ta zartar masa da hukuncin share masallacin Juma’a na tsawon kwanaki talati a jere.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zama a Unguwar Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta zartar da hukuncin sharar masallaci kan wani da ta kama da laifin sata.

Kotun ta zartar wa Halifa Abdullahi hukuncin share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki talati a jere a matsayin kudar da zai dandana ta laifin dan hali da ta tabbatar ya aikata.

Halifa wanda mazaunin Unguwar Yola ce da ke birnin Dabo, an zarge shi da balle kofar wani masallaci daren Lahadi a Unguwar Tudun Maliki, inda ya yi awon gaba da wasu Al-Kur’anai takwas a masallacin.

Bayanai sun ce masu gadin masallacin ne suka cafke matashin bayan ya aikata laifin, inda suka mika shi ofishin ’yan sanda na Filin Hoki kuma a ranar Talata aka gurfanar da shi a gaban Kuliya.

Tun a gaban Alkali matashin ya amsa laifinsa yayin da jami’in dan sanda mai gabatar da kara a gaban Kotu, Abdul Wada ya karanto laifin da ake tuhumarsa.

A kan haka ne Alkali Bello Musa Khalid ya yanke masa hukuncin share farfajiyar masallacin Juma’a na Fagge har na tsawon kwanaki talati a jere.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an yi ittifakin babu wani masallaci da ya kai na Juma’ar Fagge girma a duk ilahirin Jihar Kano.