Wata kotu a Abuja yanke wa wani barawo da aka gurfanar a gabanta hukuncin bulala 12.
Babbar Kotun Yanki da ke Zuba ta yanke hukuncin ne bayan matashin dan tiredan mai shekara 37 ya amsa laifin sata da shiga gida ba da iziniba, sannan ya nemi alkali ya yi masa sassauci.
- Halin Ni-’Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan ’Yan Gudun Hijira?
- An kama babban limamin cocin IPOB da makamai da kayan tsafi a Imo
Alkalin kotun, Gambo Garba ya ce ya yanke wa hukuncin bulala 12 ne saboda ya wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ba tare da ya wahalar da shari’a ba.
A cewarsa, da matashin ya musanta laifin da aka gurfanar da shi a kai, da ya fuskanci hukunci mai tsanani ba bulala 12 da ya yanke masa ba.
Tun da farko a zaman kotun na ranar Talata, lauyan masu gabatar da kara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa wani mazaunin layin 2nd Avenue da ke Rukuncin Gidajen Gwarimpa ne ya kai wa ’yan sanda da ke Gwarimpa rahoto a ranar 31 ga watan Yuli, 2021.
A cewarsa, matashin ya shiga gidansa ya saci tagogin karfe guda hudu sannan aka kama shi aka mika shi ga ’yan sanda kuma a yayin bincike an gano tagogin da ya sace.
Lauyan ya ce laifin ya saba wa sashi na 348 da 288 na kundin hukunta manyan laifuka.