✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wanda ya yi wa yaro fyade ya kashe shi

Kotun Daukaka Kara ta Kasar Morocco, ta yanke hukuncin kisa a kan wani matashi mai shekara 24 da ta kama da laifin garkuwa, fyade da…

Kotun Daukaka Kara ta Kasar Morocco, ta yanke hukuncin kisa a kan wani matashi mai shekara 24 da ta kama da laifin garkuwa, fyade da kashe wani yaro, dan shekara 11 a watan Satumbar bara.

Kotun da ke zaune a yankin Tangier na kasar Morocco ta kuma yanke wa abokanan zaman matashin su uku, hukuncin cin sarka na watanni hudu tare da sanya wa kowannensu tarar Dala 80.

Jami’an tsaro sun tono gawar yaron a ranar 11 ga watan Satumbar bara wanda aka binne a wani lambu mai ’yar gajeruwar tazara tsakaninsa da gidan da ’yan uwan yaron ke zama.

Matashin mai shekara 24, ya sace yaron ya kuma yi masa fyade sannan ya kashe shi a ranar 7 ga watan Satumba, ranar da ake nemi yaron aka rasa.

’Yan uwan yaron bayan sun gaji da neman shi, sun rika yada hotunansa a kwararo da lunguna domin al’umma na gari su taya su cigiya.

Al’ummar kasar ta kadu sosai da lamarin, inda cikin kankanin lokaci suka rika yada hotunan yaron a kafofin sada zumunta, lamarin da ya sanya matashin ya yi gaggawar garzayawa wajen wanzami a wani yunkuri na sauya kamanninsa domin gudun kada dubunsa ta cika.

Sai dai ba a nan gizo yake sakarsa ba, inda tun yayin faruwar lamarin, wata na’urar daukar hoto ta nadi matashin a yayin da yake tattaunawa da yaron kafin ya tafi da shi.

Jami’an tsaro sun samu nasarar gano wanda ake zargin ne bayan ya bayyana a hoton bidiyon da na’urar daukar hoton ta nada.

Yayin sauraron shari’arsa a kotu, matashin da ake zargi bai amsa laifin yi wa yaron fyade ba, sannan ya yi ikirarin cewa bai yi niyyar kashe yaron ba, sai dai kawai ya sace shi ne da nufin neman kudin fansa saboda yana da bukatar kudi.

Labarin mutuwar yaron ta girgiza al’ummar kasar Morocco da na ketare, inda har ta kai ga mabiya shafin Facebook da dama suka yi ta kiran a dawo da hukuncin kisa, wanda rabon kasar da zartar da shi tun a shekarar 1993.

Babban Limamin Masallacin Hassan II da ke Casablance, Sheikh Omar Al Kazabr, ya goyi baya ga kiraye-kirayen al’ummar kasar na neman zartar da hukuncin kisa kan laifin da matashin ya aikata na garkuwa, fyade da kisan kai.

Da dama daga cikin ’yan gwagwarmaya sun yi tsayuwar daka ta kin amincewa da hukuncin kisa, yayin da suka riki ra’ayin cewa kowane mutum yana da ’yancin ya yi rayuwa duk girman laifin da ya aikata.