Wata Babbar Kotu a Abuja ta wanke Sanata Abba Moro da wasu mutum biyu kan tuhumar da aka yi musu ta badakalar daukar ma’aikata a Hukumar Shige da Fice a 2014.
Alkalin kotun, Nnamdi Dimgba wanda ya yanke hukunci a shari’ar, ya bayyana cewa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki kasa ta’annati ta EFCC ta gaza gamsar da kotu cewa mutanen da aka gurfanar sun aikata laifukan.
- Kotu ta haramta wa ’yan jarida halartar shari’ar Nnamdi Kanu da Boko Haram
- Tsohon shugaban Burkina Faso ya samu ’yanci bayan daurin talala
Abba Moro, tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida ne a wancan lokacin, kuma an gurfanar da shi a gaban shari’a ne tare da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Shige da Fice, Mrs Anastasia Daniel-Nwobia, da wani tsohon darakta a ma’aikatar mai suna Felix Alayebami da kuma wani kamfani Drexel Tech Nigeria Ltd.
An dai tuhumi mutanen ne da hada baki su aikata lafukan da suka hada da halarta kudin haram, da kuma damfara, yayin da aka gudanar da wani aikin daukar sababbin ma’aikatan hukumar ta shige da fice.
A karshe dai rikici ya barke inda saboda wata mummunar turereniya, wasu masu neman aiki 14 suka rasa rayukansu.