✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin batanci: Kotu ta umarci ‘Legal Aid’ ta ba Abduljabbar lauyoyi

Lauyoyi na gudun kare malamin da ake zargi da yin batanci ga Manzon Allah (SAW)

Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano karkashin jagorancin Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ta bayar da umarnin rubuta wa Hukumar Agazawa Sharia ta Kasa (Legal Aid Council) da ta bai wa Abduljabbar Kabara lauyan da zai kare shi bayan da lauyoyinsa sun ayyana ficewarsu daga shari’ar.

Tun a watan Yulin shekarar 2021 Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abduljabbar Kabara a gaban kotun, bisa zargin shi da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da tayar da hankulan jama’a.

Da yake sanar da janyewar lauyoyin nasa, Abduljabbar Kabara, ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne bayan da ya rubuta takardar korafi a kansu ga wanda ya hada su da shi cewa sun saba yarjejeniyar da suka yi da shi a kan abin da za su gabatar a gaban kotun.

Haka kuma Abduljabbar Kabara ya zargi lauyoyin da yi mishi coge wajen gabatar da satifiket din kaset din karatuttukan da ya gabatar wa kotu wanda masu gabatar da kara suka yi suka a kansa a zaman da ya gabata.

“Na tuhume su da hadin baki wajen yi wa kaset din karatuttukana jabun satifiket wanda suka samo wani furoskuta a Jihar Filato ya sanya hannu a kansa, lamarin da ya sa masana shari’a suka gaya min cewa zai iya kawo min matsala a shariar,” inji malamin.

Daga nan sai kotu ta tambaye shi ko zai gabatar da wasu lauyoyin a shari’ar tasa, inda shi kuma ya ce zuwa yanzu ba shi da lauya sai dai a nan gaba.

Abduljabbar, ya shaida wa kotun cewa tun daga lokacin da lauyoyin nasa suka fice daga shariar yake ta neman lauyoyin da za su ci gaba da kare shi, amma bai samu ba.

“Kusan kashi uku ina samun lauyan da zai kare ni amma sai mun gama magana sun tafi sai su yi waya daga baya su sanar min cewa ba za su iya shiga shari’ar ba sakamakon ana yi wa rayuwarsu barazana. To hakan shi ya janyo har aka dawo kotun yau ban kai ga samun lauya ba”

Ya kuma shaidawa kotun cewa saboda haka yana neman ta ci gaba da shar’iar a haka ba tare da lauya ba domin shi ya gaji da zaman gidan gyaran hali.

“Ina rokon kotun nan ta ci gaba da shariar a matsayin zan kare kaina kafin na sami lauya.

“A maimakon na ci gaba da zama a gidan gyaran hali gara a ci gaba da shariar nan a haka, a yi abin da za a yi domin na san matsayina na huta,” inji shi.

Sai dai mai gabatar da kara, Farfesa Nasir Adamu Aliyu (SAN) ya soki rokon na wanda ake zargi, inda ya yi nuni da girman laifin da ake tuhumar shi da aikatawa, wanda ya ce wajibi ne kotun ta nuna masa illar yin shari’ar ba tare da lauya ba.

Daga nan mai gabatar da kara ya yi roko ga kotun da ta yi dayan abubuwa biyu; ko ta ba Abduljabbar dama ya dauki lauya ko kuma ta nemi Hukumar Agazawa Sharia ta Kasa (Legal Aid Council of Nigeria) da ta ba shi lauyan da zai tsaya mishi, dogaro da sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Kasa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya dauki rokon masu gabatar da kara na biyu na nema wa malamin lauyan gwamnati da zai ci gaba da kare shi a gaban kotun, inda ya kafa hujja da cewa yin hakan ma zai kawo sauri a shari’ar.

“Duk lauyan da za a bayar, wajibinsa ne ya zo kotu ko yana so, ko ba ya so, domin ma’aikacin gwamnati ne.

“Haka kuma zai tsaya ya yi aiki ba tare da korafin ana yi masa wata barazana ba; haka kuma zai jure duk wahalar shariar.

“Koda sun sami rashin fahimta da wanda yake karewa ba shi da damar ficewa daga shari’ar.

“A gefe guda kuma hakan samun sauki ne ga wanda ake tuhuma domin ba zai biya lauya ko kwabo ba; Don haka ba za mu sami wani tsaiko a shariar ba,” inji Alkali Yola.

Daga nan ya sanya ranar 26 ga watan Mayu, 2022 don ci gaba da shari’ar.