Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Sabon Gari Bola, ta umarci Sa’id Muhammad Tahar Adamu, da ya yi rantsuwa da Al-Kur’ani bayan ya gaza kare kansa daga zargin cin zarafin wani likita.
Ana dai tuhumar Sa’id wanda ɗa ne ga tsohon Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano, Dokta Muhammad Tahar Adamu da aka fi sani da Baba Impossible, da laifin dalla wa wani likita mari a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
- Gwamnatin Soji ta karya farashin shinkafa a Nijar
- Sanwo-Olu ya bullo da hanyoyi 3 na kawo wa mazaunan Legas sauƙin rayuwa
Sai dai tun a zaman Kotun na baya wanda ake tuhuma ya musanta laifin da ake zargin sa da aikatawa.
Mai gabatar da ƙara, Barista Laraba Uba, ta shaida wa kotun cewa ba su da wasu hujjojin da za su gabatar wa kotun.
Sai dai Barista Laraba ta roƙi kotun da ta sanya wanda ake zargin ya yi rantsuwa tunda ya musanta aikata laifin.
Shi kuwa lauyan wanda ake tuhumar, Barista Rabiu Abdullahi Shuaibu ya yi suka game da rokon mai gabatar da kara.
A cewar Barista Rabi’u, aikinsu ne su tabbatar da laifin da suke zargi akan wanda ake kara ta hanyar kawo gamsassun hujjoji.
Dangane da hakan ne Barista Rabi’u ya nemi kotun da ta canza ra’ayinta game da batun rantsuwar domin a cewarsa abin ya saba da Kundin Tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999.
A cewarsa “Duk wata doka da ta ci karo da Kundin Tsarin Mulkin kasa abar watsi ce kasancewar shi ne a gaba.”
Ya kuma roƙi kotun da ta yi watsi da karar kasancewar masu gabatar da kara sun gaza bayar da gamsassun hujjoji.
A kwarya-kwaryar hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Garba Malafa, ya ce kotun ta fi mayar da hankali ne game da yin adalci fiye da bin wasu hanyoyi da suka bambanta ta da kotun Majistare.
Ya kuma shawarci wanda ake kara da ya tuntubi lauyansa kafin yanke shawara kan yin rantsuwa da Al-Kur’ani.
Bayan yanke hukuncin ne Barista Rabi’u ya nemi a ɗaga shari’ar zuwa makonni biyu domin samun isasshen lokacin da za su zauna da wanda yake wakilta kan shawarar da za su yanke ta rantsuwa ko ɗaukaka kara ko kuma yin sulhu da masu ƙara.
Wakiliyarmu ta ruwaito cewa kotu ta sanya ranar 6 ga Maris don ci gaba da shari’ar.