Mai Shari’a Aisha Adamu Aliyu ta babbar kotun Jihar Kano ta umarci kwamishinan ’yan sandan jihar da ya karɓe ragamar mulki tare da fitar da sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
Umarnin na kotu ya nuna cewa, “An bayar da umarnin wucin gadi na hana mutane biyar da ake ƙara da duk wani mai alaƙa da su, su daina gabatar da kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano da Karaye har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da aka shiga a gaban kotu.
- Don maslahar Kano aka dawo da Sarki Sanusi II — Gwamnati
- An daure dan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda Fyade
“An bai wa kwamishinan ’yan sandan Kano umarnin gaggauta karɓe ragamar fadar Sarki da ke kan titin zuwa gidan gwamnati tare da fitar da wanda ake ƙara daga fadar.
Kotun ta dage sauraren ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Yunin 2024.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da sarakunan Kano Karaye, Gaya, Bichi da Rano, da aka tube da kuma, shugaban ’yan sanda, daraktan DSS, NSCDC da Sojoji.
Waɗanda suka shigar da ƙarar su ne Babban Lauyan Jihar Kano, Shugaban Majalisar Dokokin Kano da Majalisar Dokokin Jihar.
Aminiya ta ruwaito cewar Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Isah Dederi ya shaida wa BBC cewar gwamnatin jihar ta ƙarbi umarnin kotu na dakatar da tsige Aminu Ado Bayero tare da dawo da Sarki Sanusi II a ranar Litinin.