Wata kotun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta sami kasar Gini da laifin kisan masu zanga-zanga a kasarta a shekarar 2012 tare da umartarta ta biya su diyyar N1,159,740,000.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa kotun ta ba kasar watanni shida domin ta biya diyyar da yawanta ya kai Dala 510,000, kwatankwacin N193,290,000 ga kowanne daya daga cikin mutum shidan da aka kashe, yayin da kuma za a biya biliyan uku na Sefa ga dukkan mutum 15 din da aka jikkata.
- Babu kotu ko caji ofis din da aka kai ni —Rahama Sadau
- Za a yi wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS karin girma
Hukuncin wanda aka yanke shi ranar Talata ya biyo bayan zargin zubar da jinin da aka yi a watan Agustan 2012 lokacin da aka fara zanga-zanga a garin Zoghota dake Kudu maso Gabashin kasar kan wani kamfanin hakar ma’adinai na Vale-BSGR da suka zarga da nuna kabilanci a wajen daukar ma’aikata.
Daga bisani ne dai aka zargi jami’an tsaro da zuwa garin kashe-gari inda suka kashe mutum shida daga cikin masu zanga-zangar, kamar yadda kwafin takardun karar ya nuna.
To sai dai hukumomin kasar sun musanta aikata laifin, inda suka ce basu take hakkin bil-Adaman da ake zarginsu da yi ba.
Kotun dai ta yanke hukuncin cewa kasar na da hannu dumu-dumu a take hakkokin masu zanga-zangar ta hanyar azabtar da su da kuma kama wasu ba bisa ka’ida ba.
Lauyan masu shigar da karar, Pepe Antoine Lama ya ce sun yanke shawarar kai karar ne a kotun ECOWAS saboda bangaren shari’ar kasar bai nuna alamar bincikar lamarin ba.
A wani labarin kuma, Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta kasar Ginin ta ce hukuncin ya zo mata da ba-zata matuka, tana mai cewa za ta bi duk hanyoyin da suka kamata wajen ganin an yi adalci.
A watan da ya gabata ne dai aka sake zaben Alpha Conde mai kimanin shekaru 82 a matsayin shugaban kasar a karo na uku, duk kuwa da zanga-zangar da ‘yan adawa ke yi a kan hakan.