Kotun Majistare mai lamba 58 da ke zamanta a Nomansland a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Dan-Sarauniya gidan gyaran hali.
An dai gurfanar da shi a gaban kotun ne bisa zarginsa da cin zarafin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
- Ganduje na son yi wa asusun Kano karkaf —PDP
- An fara cin masu tuki suna daukar hoto tarar N100,000 a Birtaniya
Alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya bayar da umarnin yayin zaman kotun na ranar Litinin.
Kotun ta kuma dage zamanta zuwa ranar 3 ga watan Fabrairun 2022.
Tun da farko dai, lauya mai gabartar da kara Barista Wada A. Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya ci zarafin Gwamnan a shafinsa na Facebook, inda ya sa hotonsa tare da wata mata.
Hakan, a cewar lauyan na nuni da cewa Gwamnan yana neman mata a waje ke nan.
Ya ce laifukan sun saba da sassa na 392 da 399 da 114 na kundin laifuka na ACJL.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifukan da ake zarginsa da su na bata suna da tayar da hankalin Gwamna da kirkirar karya .
Lauyan wanda ake kara, Barista Garzali Ahmad ya nemi kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa sakamakon rashin lafiya da ke damunsa, wacce ya hadu da ita a daidai lokacin da ’yan sanda ke kokarin kama shi, dogaro da sassa na 168 da 172 da kuma 174.
Sai dai lauyan mai gabatar da kara ya soki batun belin inda ya ce lauyan wanda ake karar ya gaza gabatar da kwararran hujjoji akan batun rashin lafiyar wanda yake karewa, don haka ya nemi kotun da ta yi watsi da bukatar tasa.
Haka kuma ya bayyana cewa bayar da belin wanda ake kara zai zama wani abu da zai kara wa matasa kwarin gwiwar cin zarafin shugabanmi da kuma mutanen da ba su ji ba ba su gani ba
Alkalin Kotun Maisharia Aminu Gabari ya yi umarnin da a tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali na Kurmawa inda kuma ya dage zaman kotun zuwa ranar uku ga watan Fabrairu, 2022 don yin hukunci a kan batun bayar da belin.
Idan za a iya tunawa, tun a ranar Juma’a ‘yan sanda suka gurfanar da Mu’azu Magaji wanda tsohon Kwamishinan Gandujen ne a gaban kotun.
Sai dai wanda ake karar bai bayyana komai a kotun ba sakamakon ciwon kunne da yake fama da shi wanda har ya taba masa jinsa.