Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci ta daya da ke Tudun Wada, Zariya ta tura wani dagaci da masu unguwani da kuma mataimakin jami’in tsaro na Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FEC) da ke Zariya zuwa gidan yari domin zaman wakafi na mako biyu kan zarginsu da hada baki da sata da sayar da awakin talakawa.
dan sanda mai gabatar da kara Saje Adamu Yahaya ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun hada da Sarki Bello Aliyu danmasani, Dagacin Sabon Garin Gyellesu da Yusuf Aliyu Fulana Maidawa Sarkin Fulanin Gyellesu da Mai unguwa Ibrahim Umar Sabo Gyellesu da Salisu Maiwada Galadiman Dagacin Sabon Garin Gyellesu da Mataimakin Jami’in tsaro na Kwalijin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya, Mista Bitrus Sabo da wani da ake hada baki da shi yana sayar musu da awakin mai suna Tsalhatu Muhammadu Gyellesu.
dan sandan ya ce ana tuhumarsu ne da sace awakin talakawa 16, inda suka sayar da takwas a kan Naira dubu 45 suka ba matamakin jami’in tsaro na Kwalejin FCE, Bitrus Sabo Naira dubu 20 su kuma suka raba Naira dubu 25 da sauran awaki takwas a tsakaninsu.
Saje Adamu Yahaya ya ce aikata hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 139 da na 140 na kundin manyan laifuffuka na jihar. Wadanda ake tuhumar duk sun amsa laifinsu, inda Alkalin Kotun Mai shari’a Aminu Sa’ad ya tura su zaman wakafi na mako biyu kafin ya yi nazari tare da yanke hukunci a kan karar.
Wata majiya ta ce mutanen unguwar sun yi fama da sace-sacen awaki, lamarin da ya sa ’yan sintiri da jama’a suka sanya ido, inda a ranar 30 ga Agustan da ya gabata aka sanar da ’yan sintiri cewa an ga wata akuya a gidan Tsalha Muhammed, inda suka je gidan suka samu daya daga cikin awakin da aka sace, suka kai wa ’yan sanda. Majiyar ta ce da ’yan sanda suka fara tuhumar Tsalha ne sai allura ta tono garma inda ya ambaci Dagacin da masu unguwannin da mataimakin jami’in tsaro na Kwalejin FCE da hannu a lamarin.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci Kwalejin FCE domin jin ta bakin sashin tsaro da jama’ar unguwar ke zargin ma’aikatansa da hada baki ana sace musu awaki, shugaban sashin Malam Adamu Yalwa ya ce, “DPO din Tudun Wada ya gayyace ni ofishinsa domin in yi masa bayani a kan lamarin, na kuma yi masa bayani cewa awakin jama’a sun dame mu da lalata wurare tare da cinye mana shukar da muka yi domin kawata makaranta, kuma wani lokaci awakin suna shiga har cikin aji da sauran wurare su bata, don haka na yi doka cewa duk ma’aikacin da yake da gida a cikin makarantar kuma yake kiwo to ya daure abin kiwonsa, kuma na tara masu unguwannin Gyellesu da muke makwabtaka da su na roke su kan su yi shela ga jama’arsu domin su daina barin awakinsu suna shiga makarantar, amma duk da haka awakin na shiga.” Ya ce, idan suka kama awakin sai su sanar da masu unguwanni domin su kira masu awakin su ja musu kunne, kuma ya hada su da abokin aikinsa domin ganin cewa jama’a sun bi dokar, “To shi kuma sai ya hada baki da sarakunan suna bin wata hanya ta daban ba tare da sanina ba, kuma da ’yan sanda suka gayyace shi a ofishinsu ya amsa laifinsa har aka kai su kotu,’ inji shi.
Ya ce sarakuna amintatu ne na jama’a, don haka makarantar ke neman su kai-tsaye, don yin shawara da su a samu mafita kan duk abin da ya taso, amma sai aka samu akasi.