Babbar Kotun Jihar Kogi ta tsige Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga kujerarsa ta Ohinoyi na Ƙasar Ebira.
Kotun ta soke naɗin Alhaji Ahmed Muhammed ne a ranar Litinin, shekara guda bayan fara aikin basaraken.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Salisu Umar, ya kuma dakatar da basaraken daga gabatar da kansa matsayin Ohinoyi, har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.
Kotun ta bayar da umarnin ne bayan ƙarar da Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutum biyu suka shigar.
- Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano
- Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba
Sun shigar da ƙara ne suna ƙalubalantar naɗin da Gwamnan Jihar Kogi ya yi wa Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje a matsayin Ohinoyi na Ƙasar Ebira.
A watan Disamban 2023 ne tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ne ya naɗa Alhaji Ahmed Tijani Anaje a matsayin Ohinoyi na Ƙasar Ebira a yayin da tsohon gwamnan ke shirin sauka daga mulki.
A ranar 8 ga watan Janairun 2024 ne dakataccen sarkin ya fara aiki.