Kotu ta daure wani yaya da kaninsa a kurkuku saboda bindige wani manomi har lahira da suka yi.
An gurfanar da ’yan uwan biyun ne bisa zargin ta’addanci da hada baki wurin aikata kisa inda suka bindige manomin mai suna Agaba a yayin da yake hana dabbobinsu barna a gonarsa ta kashu.
- Kotu ta amince da bukatar raba aure bayan miji ya yi wa matarsa kishiya
- Kotu ta ki amincewa da bukatar kwace kadarorin Saraka.
Dan sanda mai shigar da karar, Folorunsho Zacheaus, ya shaida wa kotun cewa ana ci gaba da bincikar abin da ya auku a ranar 11 ga Fabrairu, 2021 don haka ya nemi kotun da ta ci gaba da tsare wadanda ake zargin.
Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Alkalin kotun da ke zamanta a Ilorin, Jihar Kwara, Mai shari’a Mohammed Ibrahim ya bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin Kurkuku Oke-Kura da ke, Ilorin.
Ya kuma dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 23, ga watan Maris don ci gaba da sauraren karar.