✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare wanda ya kashe matashi a gidan yari

Kotu ta tsare matashi wani matashi mai shekara 31 a gidan yari kan zargin harbe wani mai shekara 21 har lahira.

Kotu ta tsare matashi wani matashi mai shekara 31 a gidan yari kan zargin harbe wani mai shekara 21 har lahira.

A ranar Alhamis, Kotun Majistare da ke Ibadan, Jihar Oyo, ta tsare shi a gidan yari ne bayan ’yan sanda sun gurfanar da shi kan yin ajalin wani mai suna Danmagaji Sanjo.

Mai gabatar da kara, Insfekta Gbemisola Adedeji, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya harbi Danmagaji da bindiga ne da misalin karfe 10 na dare, ranar 30 ga watan Satumba, 2022, a kauyen Pondoro da ke yankin Ijio a Saki.

Ya bayyana cewa yin sanadin mutuwar mai shekara 21 din laifi ne a karkashin Sashe na 319 na Dokar Manyan Laifuka ta Jihar Oyo ta 2000.

Bayan gabatar da kara, alkallin kotun, Misis S.A. Adesina, ta ki sauraron rokon wanda ake zargin, bisa hujjar cewa kotun ba ta da hurumin yin haka.

Daga nan ta bukaci masu shiga da kara da su mika lamarin ga Ofishin Daraktan Gabatar da Kara (DPP) na jihar kan matakin na gaba.

Daga nan ta dage sauraron sharia’ar zuwa ranar 21 ga watan Disamba.