✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matashin da ya kashe matarsa da dutsen guga a Kano

Ya bayyana cewa tsautsayi ne ya sanya shi aikata abun da ya aikata, amma ya yi nadama.

Kotun majistre mai lamba 26 ta aike da wani matashi mai suna Adamu Ibrahim gidan gyaran hali bisa zarginsa da hallaka mai dakinsa ta hanyar buga mata dutsen guga a fuska.

Lamarin dai ya faru ne a garin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru ta Jihar Kano.

Tun da fari dai mijin marigayiyar ya ce sabani ne ya shiga tsakaninsa da matarsa dalilin wata mata da ta nuna ba ta son mu’amalarsa da ita.

Sai dai ya ce ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita, amma abun ya ci tura, inda ta ce babu ita babu zama da kishiya.

Daga nan ne a cewarsa ta kama shi da kokawa, kuma duk da ihun da yake yi ta ki rabuwa da shi.

Ganin haka ya sanya ya ɗauki dutsen guga akan kujera ya buga mata.

A nasa bangaren, yayan marigayiyar, Idris Adamu ya bayyana wa manema labarai cewar ba wannan ne karon farko da mijin ya ke taba lafiyar marigayiyar ba.

Idris ya ce har yaji ta taɓa yi saboda faruwar irin hakan bayan ya yi mata targade har guda huɗu a kwanakin baya.

Ya kuma ƙara da cewa har yarjejeniya suka kulla akan idan har ya ƙara dukanta, za su ɗauki mataki a kanshi.

Ƙunshin tuhumar dai na nuna a ranar 29 ga watan Afrilun ne yayan marigayiyar ya shigar da ƙorafin zargin kisan ‘yar uwarsa a ofishin ‘yan sandan Kwanar Dangora, lamarin da suka hau bincike.

Bayan kammala zaman kotun, wanda ake zargin Idris Adamu ya bayyana wa manema labarai cewa tsautsayi ne ya sanya shi aikata abun da ya aikata, amma ya yi nadama.

Kotun karkashin mai shari’a Talatu Makama dai ta sanya ranar 17 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron ƙarar.