✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matashin da ya kashe kanwarsa da matar babansa

Wata kotun majisater da ke Kano ta gurfanar da matashin da ake zargi da kisan matar babansa da kanwarsa a unguwar Rijiyar Zaki.

Wata kotun majisater da ke Kano ta gurfanar da matashin da ake zargi da kisan matar babansa da kanwarsa a unguwar Rijiyar Zaki.

Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Talatu Makama, na tuhumar matashin ne da laifin kisan kai, wanda ya saba wa sashi na 221 na kundin Penal Code.

Lauya mai kara Barista Gazali Maigari Bichi ya roki kotun ta karanto wa wanda ake tuhuma laifukansa, inda kotun ta umarci jami’inta Ibrahim Koya ya karanto masa.

Bayan karanto masa ne kuma ya amsa laifinsa, kotun ta kuma aike da shi da gidan kaso, ta kuma dage shari’ar zuwa ranar 2-3-2023.