✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare matashi kan zargin luwadi da yaro mai shekara 11 a Kano

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin

Wata kotun majistare a Kano, ta ba da umarnin tsare wani matash mai suna Nura Nuhu, a gidan gyaran hali bisa zarginsa da yin luwadi da wani yaro mai shekara 11.

‘Yan sanda sun gurfanar da matashin ne bisa laifin da suka ce ya saba wa sashe na 284 na ‘Penal Code’.

Bayan gabatar da karar, alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti ya dage shari’ar zuwa ranar biyar ga watan Yulin 2022 don ci gaba da sauraron tuhumar.

Tun farko, lauyar mai tuhuma, Asma’u Ado ta shaida wa kotun cewar Nuhu ya aikata laifin da ake zarginsa ne a ranar takwas ga watan Afrilu a unguwar Sheka Gidan Leda da ke birnin Kano.

Asma’u ta ce, Nuhu ya yaudari yaron ne zuwa wani kango inda a nan ya yi luwadi da shi.

Sai dai kuma wanda ake zargin, ya ki amincewa da aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa.

(NAN)