Wata kotun majistare a Kano, ta ba da umarnin tsare wani matash mai suna Nura Nuhu, a gidan gyaran hali bisa zarginsa da yin luwadi da wani yaro mai shekara 11.
‘Yan sanda sun gurfanar da matashin ne bisa laifin da suka ce ya saba wa sashe na 284 na ‘Penal Code’.
- ’Yan Najeriya 30,000 ke mutuwa a shekara saboda shan sigari —WHO
- Jami’ar Benin za ta fara bincike kan sarrafa makamin Nukiliya a Najeriya
Bayan gabatar da karar, alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti ya dage shari’ar zuwa ranar biyar ga watan Yulin 2022 don ci gaba da sauraron tuhumar.
Tun farko, lauyar mai tuhuma, Asma’u Ado ta shaida wa kotun cewar Nuhu ya aikata laifin da ake zarginsa ne a ranar takwas ga watan Afrilu a unguwar Sheka Gidan Leda da ke birnin Kano.
Asma’u ta ce, Nuhu ya yaudari yaron ne zuwa wani kango inda a nan ya yi luwadi da shi.
Sai dai kuma wanda ake zargin, ya ki amincewa da aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa.
(NAN)