✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matashi kan luwadi da karamin yaro a Kaduna

Kotu ta ba da umarin tsare matashin a kurkuku

Kotun Majistare da ke Kaduna ta tisa keyar wani matashi zuwa gidan yari kan zargin luwadi da wani yaro dan shekara 10.

Mai gabatar da kara, Sufeto Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya yaudari yaron ne zuwa dakinsa ya yi lalata da shi.

Ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne ran 22 ga Janairu a inda yake da zama.

A cewarsa, laifin ya saba wa Sasahe na 261 na kundin ‘Penal Code’ na Jihar Kaduna.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Emmanuel, ya bukaci a tura batun zuwa Sahshen Shigar da Kararraki na Jihar Kaduna domin neman shawara.

A karshe, Alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ran 20 ga Maris, 2023.

(NAN)