Babbar Kotun Majistare da ke zama a Ikeja, Jihar Legas, ta tsare wani matashi mai shekara 29, a gidan yarin Kirikiri saboda lalata karamar yarinya.
Dan sanda mai gabatar da kara, Christopher John, ya fada wa kotu cewar matashin ya yi wa yarinyar fyade ne a bayan ya yaudare ta zuwa gidansa.
“Yarinyar ta fada wa mahaifiyarta abun da ya yi mata, ita kuma ta kawo kara ofishin ‘yan sanda kafin aka kamo shi”, inji John.
Ya ce laifin ya saba wa sashe na 260 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas.
Mai sharia, P. E, Nwaka, ya uamrci a tsare wanda ake zargin a kurkun Kirikiri ya kuma bukaci yan sanda da su mayar da fayel dinsa zuwa ofishin shigar da kara na Jihar (DPP).
Mai Shari’a Nwaka ya kuma dage saurarar karar zuwa ranar 2 ga watan Satumba.