✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare magidanci saboda gutsire yatsun matarsa ta hanyar cizo

Wata kotun majistare dake zamanta a Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya Abuja ta ba da umarnin tsare wani bakanike,

Wata kotun majistare dake zamanta a Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya Abuja ta ba da umarnin tsare wani bakanike, Amusu Olajide bisa zargin cire wa matarsa ‘yan yatsu guda uku.

Mutumin, mai kimanin shekaru 45 wanda ke zaune a kauyen Gui a gundumar Sunka dai an gurfanar da shi gaban kotun ne tun da farko bisa zargin aikata laifukan da suka shafi yin amfani da karfi fiye da kima tare da kuma ji mata mummunan rauni.

Alkalin kotun, mai shari’a Yusuf Ibrahim a zaman kotun ranar Laraba ya umarci a ci gaba da ajiye Amusu a hannun ‘yan sanda har zuwa lokacin da za a sallami matar tasa daga asibiti.

Daga nan ne kuma ya dage zaman kotun har zuwa 18 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci.

Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara, Abdullahi Tanko ya shaidawa kotun cewa ‘yan sanda sun sami rahoton yadda wanda ake zargin ya garkame matarsa mai suna Bose mai ‘ya’ya hudu a daki bayan wata sa’insa a tsakaninsu a ranar 20 ga watan Oktoba.

Ya yi ikirarin cewa bayan yunkuri da dama na ji mata ciwo da wuka ya ci tura, Amusu ya yi amfani da hakoransa wurin gutsire wa matar tasa ‘yan yatsu guda uku.

Abdullahi ya kuma ce matar ta sami nasarar kubuta ne bayan da mai gidan da suke haya a ciki mai suna Barnabas Enoch ya kawo mata dauki.

Laifin dai a cewarsa ya saba da tanade-tanaden sassa na 265 da na 241 na kundin Penal Code.