✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare dan luwadi a kurkuku

Kotun Majistare a Jihar Kebbi ta tsare wani mutum da ake zargi da yin luwadi da wani karamin yaro. An gurfanar da mutumin mai shekara…

Kotun Majistare a Jihar Kebbi ta tsare wani mutum da ake zargi da yin luwadi da wani karamin yaro.

An gurfanar da mutumin mai shekara 19 ne bayan zarginsa da yi wa yaron dan shekara 10 fyade a Karamar Hukumar Jega ta jihar.

Dan sanda mai gabatar da kara ya ce an kame wanda ake tuhumar ne bayan ya lalata yaron a ranar biyu ga watan Yuli.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Diri ya umarci a tsare wanda ake tuhumar a gidan yari, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.