✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tabbatar da takarar Adamu Aliero a PDP

A yanzu Sanata Adamu Aliero zai fafata da Gwamna Atiku Bagudu na jam'iyyar APC.

Kotun Koli ta tabbatar da Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin dan takarar kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

A ranar Litinin ne tawagar alkalan kotun biyar karkashin jagorancin mai shari’a China Centus Nweze, suka yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara da na Babbar Kotun Tarayya suka yanke a baya, a kan zaben fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar.

Alkalan sun yanke hukuncin cewa kalubalantar ayyana Sa’idu Haruna a matsayin dan takarar Sanata a jam’iyyar PDP yana kan daidai.

Haka kuma Kotun Kolin ta tabbatar da zaben Dakta Abubakar Yahaya Abdullahi a matsayin dan takarar Sanatan Kebbi ta Arewa a karkashin jam’iyyar PDP.

A yanzu Sanata Aliero – wanda tsohon Gwamnan Jihar Kebbi ne – zai fafata da Gwamnan Jihar mai ci Atiku Bagudu, wanda ke takarar kujerar Sanatan a jam’iyyar APC mai mulkin jihar.