Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta tabbatar da na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso, wato Shehu Wada Sagagi, a matsayin halastaccen Shugaban PDP a Jihar Kano.
Sagagi dai na da kusanci da Kwankwaso, wanda yanzu haka shi ne dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP bayan ya bar PDP a watan Maris.
- Kaso 2 bisa 5 na kudin ’yan Afirka a abinci yake tafiya’
- Dino Melaye ya sha kaye a zaben fid da gwanin Sanata a Kogi
A ranar 17 ga watan Mayu ce dai alkalin kotun, Mai Shari’a A. M. Liman ya ba da umarnin wucin gadi na dakatar da shugabancin jam’iyar karkashin jagorancin Sagagi har sai an kammala zaman kotun.
Bello Bichi ne dai ya shigar da karar inda yake karar Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), jam’iyar PDP, da karin waau mutum 40.
Da yake janye wancan umarnin na baya, alkalin ya ce mai kara ya bata wa kotun lokaci bisa nuna mata akwai bukatar daukar matakin gaggawa kan lamarin.
Kazalika alkalin ya ce mai karar ba shi da hurumin shigar da ita, domin ya gaza gabatar da shaidar da ke nuna shi dan kwamitin zartarwar jam’iyyar ne.
Daga nan ne sai ya dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Mayu mai zuwa.