Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta ayyana Julius Abure, a matsayin Shugaban Jam’iyyar LP na ƙasa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya tabbatar da jagorancin Abure da taron jam’iyyar da aka gudanar a Nnewi a watan Maris 2024 wanda ya kafa shugabancin jam’iyyar.
- Ilimi: Kwankwaso ya taya Abba murnar lashe lambar yabo ta NUT
- Gwamnatin Tarayya ta daina biyan tallafin kuɗin aikin hajji
Har wa yau, kotun ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta amince da Abure a matsayin shugaban jam’iyyar duk da cewa INEC ba ta amince da shugabancin ba.
INEC, ta yi iƙirarin cewa taron LP da aka gudanar a Jihar Anambra, an yi sa ne ba bisa ka’ida ba, kuma ta ce wa’adin Abure zai ƙare a watan Yunin 2024.
Saboda haka, wasu ’ya’yan jam’iyyar, ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da Gwamna Alex Otti, sun gudanar da taro inda suka naɗa Misis Nenadi Usman a matsayin shugabar kwamitin kulawa da za ta warware matsalolin jam’iyyar.
Sai dai tsagin Abure ya kira taron gaggawa da kuma ƙin amincewa da naɗin nata.
Bayan hukuncin kotun, Abure ya bayyana farin cikinsa da nasarar da ya samu.
Ya gode wa Allah kuma ya yaba wa Mai Shari’a Nwite kan hukuncin da ya yanke cikin adalci, wanda ya yi imanin hakan zai dawo da ƙimar harkar shari’a.
Abure ya ce ya yafe wa waɗanda suka yi ƙoƙarin rage durƙusar sa shi da kuma jam’iyyar, inda ya yi fatan za su fahimci kuskurensu su kuma yi sulhu da jam’iyyar.
Kazalika, ya yi kira ga Peter Obi da su haɗa hannu don ci gaban jam’iyyar.