Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta a ranar Alhamis ta soke nasarar Da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya samu.
A sakamakon haka, kotun ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
- An ‘harbi’ masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Kaduna
- Gobe kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano
Kotun dai ta ce za a sake zaben ne a wasu Kananan Hukumomin Jihar guda uku.
Kananan Hukumomin su ne Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukyun.
A cewar kotun, hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan ya yi a baya, wanda ya tabbatar da nasarar Dauda, bai yi la’akari da hujjar da jam’iyyar APC mai kara ta gabatar ba.
Kazalika, kotun ta yi fatali da sakamakon da APC da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayar a Karamar Hukumar Maradun.
Tsohon Gwamnan Jihar, kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle ne dai ya shigar da karar yana neman a soke nasarar Dauda a zaben.
Hukumar INEC dai ta bayyana Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.