Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta soke zaben fid-da gwanin jam’iyyar PDP a kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya.
Kotun dai ta yanke hukuncin ne ranar Laraba saboda ta ce ba a bi ka’ida ba wajen gudanar da zaben.
- Mutum 2 sun gurfana a gaban kotu kan zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci
- Kyankyaso: Kwaron da ke iya rayuwa tsawon mako daya babu kai
Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammed Umar, ya kuma umarci PDP da ta sake shirya sabon zabe cikin kwanaki 14 masu zuwa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar, Usman Ibrahim, ta hannun lauyansa, Samuel Atung, ne garzaya gaban kotun yana kalubalantar nasarar da Lawal Adamu ya samu a zaben.
Wanda yake karar, ya kalubanci zaben ne saboda an kada kuri’un da suka wuce ka’ida a zaben, inda ya nemi kotun da ta soke shi domin a ba kowa damar gwada farin jininsa.
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Muhammed ya ce dukkan hujjojin da mai kara ya gabatar wa kotun masu inganci ne, sannan matakin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dauka na shirya wani sabon zabe bayan wanda ake karar ya yi mata wata da’awa shi ma ba yanzu ta rushe shi.
Da yake tsokaci a zantawarsa da manema labarai jim kadan da yanke hukuncin, lauyan mai kara, Samuel Atung, ya ce hukuncin ya nuna cewa kotu ita ce gatan karshe ga mai karamin karfi.