Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kasafin kudin Jihar Ribas na Naira biliyan 800 na shekarar 2024 da Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar.
Da yake yanke hukunci a safiyar Litinin, Mai Shari’a James Omotoso ya ce kasafin da gwamnan ya gabatar a gaban mambobi hudu na majalisar da ke tsaginsa, haramtacce ne.
Don haka ya umarci gwamnan ya sake gabatar da kasafin a gaban halastaccen zauren majalisar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, daga tsagin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rikicin Wike da Fubara ya raba kan majalisar dokokin jihar, inda akasarin mambobin suke bangaren Wike suka kuma sauya sheka zuwa APC, har suka tsige sohon shugaban majalisar suka nada daya daga cikinsu.
- Matsalar tsaro: Wike ya ki sauraron Sanatar Abuja
- Mutum 16 sun mutu a hatsarin mota a hanyar Kano-Kaduna
Gwamnan ya rike kudaden majalisar sannan ya sauya wa magatakardan majalisan da mataimakinsa wurin aiki, a matsayin martinsa kan baren ’yan bangaren Wike.
Amma alkalin ya sanar cewa gwamnan ba shi da hurumin hana majalisar dokokin jihar kudadenta.
Daga nan ya yi wa gwamnan gargadi game da yunkurin kawo cikas ko yin katsalandan ga harkokin gudanar da majalisar da Amaewhule ke jagoranta.
Alkalin ya kuma soke sauyin wurin aiki da gwamnan ya yi wa magatakardan majalisan da mataimakinsa.