Babbar Kotun Jihar Kano ta ɗage yanke hukunci a kan buƙatar dakatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ci gaba da aikin gudanar da gyare-gyare a ƙaramar Fadar Nassarawa.
Kotun ƙarƙashin jagorancin Babbar Jojin Kano, Mai Shari’a Dije Aboki ta tsayar da ranar 10 ga watan Oktoba domin yanke hukunci a kan buƙatar.
Haka kuma, ta ba da umarnin liƙe dukkanin shari’o’in da ke da nasaba da wannan a alon fidda bayanan kotun domin tabbatar da cewa an sanar da dukkanin bangarorin da ke cikin shari’ar game da halin da ake ciki.
Masu kara, da suka hada da Gwamnatin Kano da Antoni Janar na Kano da Majalisar Masarautar Kano, ta hannun lauyansu, Rilwanu Umar (SAN), sun buƙaci a bar fadar a yadda take domin adana tarihi da al’adu, inda suke tirjiya a kan zamanantar da ita.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Satumban da ya gabata ne Mai Shari’a Dije Aboki ta bayar da umarnin hana Sarki Bayero, yi wa ginin Fadar Nassarawa kwaskwarima.
Wannan taƙaddamar dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun saɓata juyata tsakanin ɓangarensa da kuma Gwamnatin Kano wadda ta dawo da Sarki Muhammad Sanusi II, bayan rushe masarautun jihar guda biyar da majalisar dokoki ta yi.
Sarki Aminu dai ya mayar da Fadar Nassarawa matsuguninsa, inda yake ci gaba da ƙafafa da gudanar da harkokinsa a matsayin sarki mai cikakken iko.