Babbar Kotur Tarayya da ke Abuja ta sake yin fatali da bukatar da lauyoyin dakataccen dan sanda, DCP Abba Kyari, suka sake gabatar mata kan bayar da belin shi.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ya ce lauyoyin ba su ba da gamsassun hujjojin da za su sa kotun ta amince da bukatar wanda suke karewa din ba.
- Kotu ta daure mutumin da ya kashe kaninsa
- Bayan umarnin Buhari, sojoji na samun nasara kan ’yan ta’adda
Tun da farko dai, lauyan Abba Kyari, Chuba Ikpeazu (SAN), ne ya kawo bukatar bayar da belin saboda zargin da ya yi na barazanar da ma’aikatan gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja na yi wa rayuwar wanda yake karewa.
Lauyan ya ce bukatar ta zama dole saboda Abba Kyarin da abokan aikinsa da dama sun taka muhimmiyar rawa wajen da yawa daga cikin wadanda ake zargin yayin aikinsa na dan sanda.
An dai gurfanar da shi ne tare da ACP Sunday Ubua da ASP Bawa James da kuma Insfekta Simon Agirigba da Insfekta John Nuhu, sai kuma ASP John Umoru, wanda yanzu haka ya tsere.
Ana dai zarginsu ne da hada-hadar miyagun kwayoyi.
Kazalika, Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kuma gurfanar da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne bisa zargin hada-hadar kwayoyin.
Tuni dai kotun ta daure su bayan sun amsa aikata laifukan da ake zarginsu da yi.
Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranakun 19, 20 da kuma 21 ga watan Oktoban 2022.