Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran IPOB, kungiyar ’yan aware masu fafutikar kafa kasar Biyafara.
Kotun ta ce ta dage shari’ar zuwa Laraba don bai wa lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu damar yin nazari kan sababbin tuhume-tuhume 15 da GwamnatinTarayya ta shigar a kansa.
- Ramuwar gayya: Sojojin Larabawa sun kashe mayakan Houthi 11 a Yemen
- FIFA ta fitar da tawagar fitattun ’yan wasanta na 2021
Sai dai Nnamdi Kanu bai ce ya amince da tuhume-tuhumen ba kuma bai ce bai amince da su ba bayan an karanto masa su.
Lauyoyinsa sun shaida wa kotun cewa wanda suke karewa ba zai iya cewa komai ba har sai sun yi nazarin tuhume-tuhumen.
A jiya Litinin ne Gwamnatin ta sake gabatar da sababbin tuhume-tuhume har guda 15 kan Nnamdi Kanu, kari a kan guda bakwai da tun da farko aka gabatar masa.