Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta sake sanya ranar 27 ga watan Yulin 2022 don sauraron karar da lauyan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar yana neman a yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Malamin, wanda yanzu haka yake fuskantar shari’a a kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a birnin na Kano dai na neman wannan kotun ta waccan ci gaba da gudanar da shari’ar da ake yi wa wanda yake karewa.
- Zaben 2023 zai fi kowanne inganci a tarihin Najeriya — INEC
- An tsinci gawar malamin cocin da ’yan bindiga suka sace a Kaduna
Tun da farko, lauyan Sheikh Abduljabbar, Barista Dalhatu Shehu Usman ya garzaya gaban kotun don neman ta bayar da oda game da tuhumar da ake yi wa wanda yake karewa a kotun kasa, inda ya kalubalanci kotun cewa tuhumar da ake yi wa Abduljabbar din ba ta bisa ka’ida.
Lauyan ya kuma bukaci kotun ta dage masa shari’ar kasancewar bai sami takardun martanin lauyoyin gwamnati a kan lokaci ba, ballantana ya iya mayar da nasa martanin.
Sai dai Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdullahii Muhammad Liman, ya ki amincewa da bukatar lauyan na Sheikh Abduljabbar, lamarin da ya janyo lauyan ya nemi ya janye karar gaba daya.
Sai dai da aka waiwayi lauyoyin gwamnati, sun nuna rashin jin dadinsu a kan janyewar da lauyoyin Abduljabbar din suke yawan yi a duk lokacin da suka shigar da kara, inda suka nemi a yi musu gargadi akan hakan tare da neman diyyar Naira dubu 200.
A cewar lauyan gwamnatin Kano, “Wannan shi ne wajen karo na hudu suna shigar da kara a kan batun take hakkin wanda ake yi wa shari’ar sannan daga baya su janye.
“To don haka a sanya sharadi kada su sake shigar da makamanciyar wannan kara. Muna neman su biya mu diyyar Naira dubu 200 saboda bata mana lokaci da suka yi,” inji shi.
Daga nan Alkalin kotun ya amince da ya kara wa Lauyan Abduljabbar Kabara lokacin da zai iya mayar da martani kan kunshin bayanan lauyoyin gwamnatin da suka mika masa a safiyar wannan rana.
Tun a makon jiya ne lauyan na Abduljabbar, Barista Dalhatu Shehu Usman ya garzaya gaban kotun Tarayyar yana neman oda daga kotun wacce za ta hana kotun Shari’ar Musuluncin ci gaba da tuhumar da take yi wa wanda yake karewa.