Wata Babbar Kotu mai zamanta a Jihar Edo, ta yanke wa wata ’yar aiki hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ta same ta da laifin kashe mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Edo, Chief Lucky Igbinedion.
’Yan sanda sun gurfanar da ’yar aikin mai suna Dominion Okoro tare da wata ’yar uwar marigayiyar a kotu bisa zargin kashe Misis Maria Oredola Igbinedion ne tun a Disamban 2021.
- Limamin Masallacin Maiduguri Road Kaduna ya rasu
- Matashi zai shafe wata 8 yana wanke ban-daki kan laifin damfara a intanet
’Yan sandan sun shaida wa kotun cewa, Dominion ta kashe uwargijiyarta Misis Igbinedion ne a ranar daya ga Disamban 2021, a gidanta da ke yankin Ugbor a Benin don ta samu damar sace mata kudi N100,000.
Da take bayani kafin zartar da hukuncin, Alkalin kotun, Mai Shari’a Efe Ikponmwoba ta ce, masu gabatar da kara sun gabatar wa kotun gamsassun hujjoji kan batun.
Bayanan ’yan sanda sun nuna cewa, bayan da Dominio ta kashe mahaifiyar tsohon Gwamnan ta hanyar kwala mata wata ’yar kujera, kashegari sai ta tsere ta bar gidan.
Kotun ta ce bayan gamsuwa da duka hujjojin da aka gabatar mata daga bangarori daban-daban, ta yanke wa mai laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A karshe, kotu ta kuma wanke ’yar uwar marigayiyar, Patience, wadda aka gurfanar da su tare da Dominion bayan ta gamsu cewa Patience ba ta da hannu a mutuwar ’yar uwarta ba.