Wata kotun al’ada dake Ibadan na jihar Oyo ta raba auren shekaru hudu tsakanin Abosede Adesonwo da mijinta, Wasiu bisa zargin shaye-shayen giyar ta na barazana ga rauwarsa.
Da yake yanke hukuncin a ranar Talata, alkalin kotun, Mai Shari’a Cif Henry Agbaje ya ce kotun ta yanke shawarar raba auren ne saboda a sami zaman lafiya da maslaha.
Alkalin ya kuma ba matar umarnin ta ci gaba da kula ’yar da suka Haifa guda daya, yayin da shi kuma mijin nata Wasiu zai rika biyan N5,000 a kowanne wata domin kula da ’yar da kudin abincin ta a kowanne wata.
Tun da farko dai, Wasiu wanda mai sana’ar yin burodi ne ya zargi matar da kasancewa rikakkiyar ’yar giya.
Ya ce, “Ta na ba ’yar da muka Haifa mai kimanin shekaru uku da rabi giya. Ban taba sanin cewa ’yar giya ba ce kafin mu yi aure.
“Yanzu ta nuna min hakikanin halin ta,” inji Wasiu.
A nata bangaren kuwa, matar, wacce ’yar kasuwa ce ta ce ta yanke shawarar datse igiyar auren ne saboda mijin ya kan lakada mata duka a kai a kai.
“Aure na da shi bai da wani amfani, ya kan doke ni wasu lokutan. Ya kuma taba yin barazanar kashe ni,” inji ta.