A ranar Litinin, wata kotun majistare dake zamanta a Ibadan a jihar Oyo ta raba auren shekaru 12 tsakanin wani manomi, Wasiu Oladosu da matarsa Amdalat saboda zargin matar na da saurin fushi.
Da yake bayar da shaida a gaban kotun, Wasiu ya ce kusan kullum matar sai ta yi fada da abokiyar zamanta saboda saurin fushinta.
- Ya gurfanar da matarsa a gaban kotu bisa zargin yunkurin kashe shi
- Magidanci ya caka wa matarsa wuka a kotu a Kano
Dagan nan ne sai shugaban kotun, Mai Shari’a Ademola Odunade ya yanke hukuncin raba auren saboda a sami zaman lafiya.
Sai dai ya ba matar damar ci gaba da kula da ’ya’yan da suka Haifa, inda shi kuma mijin ta umarce shi da ya rika biyanta N20,000 a kowanne wata a matsayin kudin abinci da kula da su.
Kazalika, kotun ta umarci Wasiu da ya biya matar da ’ya’yan nata kudin hayar gidan da za su zauna har na tsawon shekara daya
Tun da farko dai Wasiu ya shaidawa kotun cewa, “Amdalat ta san ina da wata matar bayan ita. Ta kan yi matukar kishi a duk lokacin da nake tare da waccan matar.
“Ta kan zage ni hatta a bainar jama’a. Akwai lokacin ma da ta watsa min ruwa ni da matar tawa saboda tana fushi da ni,” inji Wasiu.
Sai dai da take mayar da martani, Amdalat ta ce ba ta goyon bayan a kashe auren nasu saboda har yanzu tana son .
Ta ce, “Miji na sam baya yi min adalci. Yana wulakanta ni kuma ya fi kasancewa tare da waccan matar a lokuta da dama.
“Ni dai iyakar abinda na sani shine ina son Wasiu da zuciya daya. Amma shi sam ba ya nuna min son saboda waccan matar,” inji Amdalat.