Wata kotun majistare dake zamanta a yankin Mapo a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta raba auren shekaru 12 tsakanin wasu ma’aurata saboda mijin ya ki ya nemi sana’a don kula da iyalansa.
A cikin karar da matar mai suna Itunun Osin wacce take sana’ar kitso ta shigar ta roki kotun da ta datse igiyar auren da tsohon mijin nata mai suna Kehinde saboda ta ce ragon maza ne kuma ba ya iya daukar nauyin iyalansa.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, mai shari’a Ademola Odunade ya ce kotun ta yanke shawarar raba auren ne saboda ma’auratan sun ki su zauna lafiya da juna.
Ya kuma ba matar umarnin ta ci gaba da rike ‘ya’yansu yayin da shi kuma Kehinde zai ci gaba da biyan N10,000 a kowanne wata a matsayin kudin kula da su.
Alkalin ya kuma umarci mijin ya biya tarar N20,000 saboda lalata wayar tsohuwar matar tasa.
Tun da farko dai matar ta yi zargin cewa mijin nata malalaci ne.
Ta ce, “Ya ki ya nemi aiki. Har bashi na karbo masa a banki domin ya fara sana’a amma a karshe ya watsa min kasa a ido ta hanyar turmushe kudin ya kuma kyale ni da biyan bashin ni kadai.
“Mai shari’a, Kehinde har duka na yake yi. Ya farfasa min sabuwar wayar da na saya mai tsada kafin na bar gidansa a watan Nuwamban 2019,” inji ta.
Sai dai wanda ake zargin ya amsa duk zarge-zargen da ta yi masa, ko da dai ya ce yana da dalilin aikata hakan.
Kehinde wanda dan acaba ne ya ce sam Itunun ba mace ta gari ba ce.
“Tana neman maza. Na kuma fasa wayarta ne da gangan saboda tana kiran samarinta da ita a gaba na ba kunya ba tsoron Allah,” inji Kehinde.