Wata kotu dake zamanta a Ile-Tuntun a Ibadan ta raba auren shekara 15 tsakanin Adeyemi Bamigbola da Bidemi, kan zargin cin amana.
Mai shari’a Cif Henry Agbaje ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, don kawo karshen tashin-tashina a tsakanin ma’auratan.
- Kotu ta raba auren shekaru 4 saboda an gano matar ’yar giya ce
- Matar aure ta kashe dan kishiyarta
- An daure shi a gidan yari saboda zagin tutar China
- Kotu ta daure matar da ta jagoranci yaki da hana mata tuki a Saudiyya
Bayan raba auren, alkalin kotun ya umarci Bamigbola da yake bai wa matar dubu goma duk wata domin kula da yaransa guda biyu.
Tun farko Bamigbola ne ya shigar da kara gaban kotun, inda ya bukaci ta raba aurensa da matarsa, saboda neman maza da take yi.
Ya ce “Jami’an ‘yan sanda a Oyo sun taba kama mata da wani saurayinta mai suna Jomo suna aikata fasikanci.”
Da take maida martani, Bidemi, wacce ‘yar kasuwar ce, ta ce “Bamigbola ba mutum kirki ba ne don ko daukar dawainiya ta da yaranmu ba ya yi.”
“Akwai lokacin da aka taba yunkurin korarmu daga gidan haya, saboda ya gaza biya sai bashi na karbo na biya kudin hayar.”
Kazalika, ta koka kan yadda mijin nata yake shan giya da bin matan banza.
Ta ce, “na sha kama shi da matan banza a kan gadonmu na aure.”
Saboda wannan tirka-tirka da aka dinga fama da ita kotun, ta yanke hukuncin raba auren don samun masalaha.