Wata kotu da ke zamanta a Jos, babban birnin Jihar Filato, ta raba auren shekara 10 saboda gazawar wani magidanci wurin samar da abinci ga matarsa.
Tun da fari matar ta shigar da kara a kotun, inda ta bukaci a raba aurenta da mijin nata sakamakon gaza daukar nauyin aure da yake kansa.
- Atiku: Ruwa ba sa’an kwando ba ne – Sakon PDP ga Tinubu
- An kama uwa da ’yarta kan antaya wa wata mata ruwan zafi
Har wa yau ta yi alkawarin mayar mishi da sadakin da ya biya lokacin da ya aure ta N20,000, idan har ba zai sake ta cikin ruwan sauki ba.
Tuni dai kotu ta bayar da umarnin hakan, tunda ma’auratan sun gaza yin sulhu a tsakaninsu.
Alkalin kotun, Ghazali Adam, ya raba auren sannan ya umarci matar da ta mayar wa tsohon mjin nata da sadakin da ya biya.
Kazalika, ya umarci mijin da ya rika bai wa tsohuwar matar N20,000 duk wata don kula da ’yarsa mai shekara hudu a duniya.