Wata kotun al’ada da ke yankin Igando a Jihar Legas, ta raba auren wasu ma’aurata saboda yadda matar ta gudu kasar Kanada neman kudi, ba da izinin mijin nata ba.
Kotun dai wacce ta yanke hukuncin ranar Talata ta ce ta yi hakan ne bayan gamsuwa da hujjojin da mijin, mai suna Sheriff Lawal, ya gabatar a gabanta.
- An gano gawar mutum 4 a fashewar tukunyar gas a Kano
- Jirgin kasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki ranar Litinin
Alkalin kotun, Mai Shari’a Adeniyi Koledoye, ya ce, “Tun da aka fara zaman kotun nan, matar ba ta bayyana ba saboda ba ta Najeriya. Amma dai kotun ta gamsu cewa tana sane da shari’ar ita da danginta.
“Bisa la’akari da hujjojin mai kara, wadanda su kadai ne muka samu, wannan kotun ta gano cewar matar ta gaji da auren nan.
“Matukar hat za ta iya barin gidan aurenta ba tare da izinin mijinta ba, wanda bai ma san inda take ba, sai daga baya ya gano ta tafi kasar waje, hakan na nufin babu ragowar soyayya a tsakaninsu,” inji alkalin.
Ya yanke hukuncin cewa kowane daga cikin ma’auratan zai iya kama gabansa tun da dama babu haihuwa a tsakaninsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Sheriff, wanda yake sana’ar walda na zaune ne a kan titin One Day Avenue da ke Egan a Jihar.
Ya garzaya gaban kotun ne tun da farko yana neman a datse igiyar aurensu saboda zargin wasa da aure rashin soyayya da kuma yawan yin karya da yake zargin tsohuwar matar tasa da aikatawa.
“Danginta ma ba su ce mun uffan ba duk da cewar sun san ta gudu, na fahimci babu ragowar soyayya a tsakaninmu, shi ya sa na garzaya kotun ina neman a raba auren,” inji mijin. (NAN)