✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta raba aure saboda masifar mata

Kotun dai ta amince da raba auren saboda masifar matar

Wata kotun majistare  da ke Ado-Ekiti ta cika wa wani magidanci mai suna Ibrahim Idris burinsa, bayan da ta raba aurensu da matarsa Bosede kamar yadda ya bukata.

Idris ya bukaci kotu ta raba auren nasu ne saboda rashin girmama shi da kuma masifar da ya ce tana yi mishi, ta yadda a kan abun da bai taka kara ya karya ba sai ta hau shi da fada.

Bayan cikakken nazarin karar da aka gabatar mata, daga bisani Alkalin kotun, Misis Foluke Oyeleye ta kashe auren ma’auratan.

Daga nan, Alkalin ta yanke hukunci ‘yar da suke da ita ta ci gaba da zama a hannun Bosede, sannan ta umarci Idris ya dauki nauyi ‘yar a matsayinsa na mahaifinta.

Haka nan, ta ba da umarnin a saka ‘yar a makarantar Islamiyya, kana uban na da damar ya ziyarce ta a makaranta a duk lokacin da ya bukaci hakan.

Bayan haka, ta sake dora wa Idris nauyin mika kudi N10,000 duk wata, a matsayin kudin kula da ‘yar da ma abincinta.

Idris ya fada wa kotun cewa, “Sam, ba na samun kwanciyar hankali, ba ta daukar gyara sannan takan yi mini barazana.

“Ina sauke hakkokin da suka rayata a kaina a matsayina na miji kuma uba.

“Ina bukatar ‘yata ta zauna a hannuna saboda ina so ta tashi a cikin Musulunci, kuma ta rika zuwa makarantar Islamiyya, kamar sauran ‘ya’yana,” inji magidancin.

Sai dai, Bosede ta karyata duka zargin da maigidanta Idris ya gabatar wa kotun.

A karshe, Bosede ta roki kotun a kan ta kwato mata wasu kayayyakinta da ke hannun Idris tun da aurensu ya mutu.

(NAN)