✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta mallaka wa gwamnati Naira biliyan 12 da suke da alaka da Patience Jonathan

Wata Kotun Tarayya da ke Legas ta mika wa Gwamnatin Tarayya Dala miliyan 8.4 da kuma Naira biliyan 9.2 da suke da alaka da matar…

Wata Kotun Tarayya da ke Legas ta mika wa Gwamnatin Tarayya Dala miliyan 8.4 da kuma Naira biliyan 9.2 da suke da alaka da matar tsohon Shugaban Kasa, Misis Patience Jonathan.

Alkalin Kotun, Mai shari’a Mojisola Olaterogun ce ta ba da wannan umarni, ta ce ba a kawo wani dalili ba, da ba za a mika kudin ga gwamnati ba. Kotun ta ce kudaden wadanda Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) take zargin na sama da fadi ne, wanda kuma hakan laifi ne da ya saba wa sashin na 17 na hana cuwa-cuwar kudade da sauran laifuffuka da suka jibanci haka.

A ranar 20 ga watan Afrilu 2018 ne, Hukumar EFCC ta nemi izinin kwace wadannan kudade na wucin-gadi bayan koken da ta shigar a gaban kotu, a kan Patience Jonathan da kuma wasu kamfanoni da suka hada da Globus Integrated Serbices Ltd da Finchley Top Homes Limited da Am-Pam Global Network Limited da Pagmat Oil and Gas Limited da kuma Magel Resort Limited and Esther Oba. A ranar 29 ga watan Oktoba bara, Lauyan Hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo ya gabatar da bukatar a kwace kudaden a kuma mika su ga Gwamnatin Tarayya.

Sai dai kuma lauyoyin masu kare wacce ake kara, Ifedayo Adedipe (SAN) da Mike Ozekhome (SAN) da Ige Asemudara sun kalubalanci wannan mataki na kwace kudaden kwata-kwata.

Tun a ranar 5 ga watan Janairun bana ce ayarin lauyoyin hukumar suka gabatar wa kotun wata shaidun ta suke nuni da irin harkokin kasuwanci da aka gudanar a kamfanonin Finchley Top Homes Ltd da kuma na Magel Resort Limited.

A hukuncin da kotun ta yanke a watan Fabrairun bana, ta ce ba ta gamsu da waccan shaida da aka gabatar mata ba, domin akwai shakku a kai don, haka a gabatar da bayanai da baki daga dukkan sassan biyu. Sai kotun ta bad a umarni ga dukkan sassan biyu su kira shaidunsu. A zaman karshe na dage karar wani mai ba da shaida na Hukumar EFCC, Orji Chukwuma ya gabatar da shaidarsa, inda a karshe kotun ta tabbatar da cewa dukiyar ta cuwa-cuwa ce.