Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta kwace masallatai da litattafan Abduljabbar Kabara guda 189, bayan ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin yin batanci ga Manzon Allah (SAW).
Kotun da ke zamanta a Kofar Kudu a birnin Kano ta ba da umarni kai litattafan malamin zuwa dakin karatu na Gwamnatin Jihar Kano.
- Za a rataye matashiyar da ta kashe makwabciyarta a Kano
- A gaggauta yanke min hukuncin kisa —Abduljabbar
Ta kuma sa Gwamnatin Jihar Kano ta kwace masallatansa guda biyu — Asshabul Kahfi da ke unguwar Gwale da kuma Jamiur Rasul da ke unguwar Sabuwar Gandu.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya kuma haramta sanya karatuttuka ko hotunan Abduljabbar ta kowace kafar yada labarai wanda.
Sannan ya ba ba da umarnin kamawa da kuma hukunta duk wanda ya saba wadannan umarnin.
Alkalin kotun ya yi kira ga malaman Jihar Kano da babbar murya da su rika zabar kalamai masu kyau wajen bayyana ra’ayyoinsu ga dalibansu don gudun jefa alumma cikin halaka.