Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamna da na ’Yan Majalisar Dokoki a Jihar Gombe ta soke zaben Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Abubakar Muhamamd Luggerewo.
Shugaban Majalisar dai an zabe shi ne a karkashin Jam’iyyar APC mai mulkin jihar domin wakiltar mazaɓar Akko ta Tsakiya.
- ’Yan sanda sun far wa wakilan Aminiya da BBC a kotun zaben gwamnan Kano
- KAI-TSAYE: Yadda kotu ke yanke hukunci kan zaben Gwamnan Kano
Sai dai babban abokin hamayyar sa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Bashir Abdullahi, ya kalubalanci nasarar zaben nasa a kotu inda hakan ya jawo rushe zaben.
Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Michael Ugar ta soke nasarar ne saboda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soke kuri’un da aka kada a wasu rumfunan zabe a mazabar, wanda mai shigar da kara ya koka a gaban kotun cewa matakin ne ya bai wa wanda ake kara nasarar da ba ta dace ba a zaben na ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Mai shari’a Ugar ya ce soke sakamakon zaben rumfuna masu lamba 001, 024 da 014 na garin Kumo ta Gabas a Ƙaramar Hukumar ta Akko kuskure ne, inda nan take ta bai wa hukumar NEC umarnin ta sake gudanar da zabe cikin kwanaki 30 masu zuwa don tantance ainihin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar.
Sai dai shugaban majalisar, Abubakar Muhammad Leggerowo ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke, kuma ya sha alwashin daukaka kara a gaban kotun daukaka kara cikin gaggawa.