Wata kotu a Brazil ta bayar da umarnin a kwace kadarorin da shahararren dan kwallon FC Barcelona Neymar da Silba Santos Junior ya mallaka a kasar saboda samunsa da laifin kin biyan haraji.
Kamar yadda wata jaridar da ake wallafa wa a Brazil ta ruwaito an ce kotun ta bayar da umarnin a kwace kadarorin dan kwallon ne da suka kai Dala miliyan 50 kwatankwacin Naira Biliyan 16 da miliyan 250 a bisa laifin rashin biyan haraji na wadansu shekaru da bai yi ba..
Rahoton ya ce kotu ta kwace kadarorin dan kwallon ne da suka hada da jirgin ruwa da jirgin sama da asusun ajiyar banki da kuma wadansu daga cikin gine-ginen da ya mallaka da aka kiyasta kudinsu sun kai Dala miliyan 16 amma Neymar da iyalansa da gangan suka ki biyan haraji a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013 da yin haka babban laifi ne a kundin tsarin mulkin kasar.
Wata kotu da ke Sao Paulo ta yi watsi da karar da dan kwallon ya shigar a makon jiya a yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kwace masa kadarori. Bayan watsi da karar ce sai jami’an tsaro suka kwace kadarorin da dan kwallon ya mallaka.
Wani jami’in yin bincike kan yadda ake biyan haraji a kasar Lagaro Jung Martins ya ce abin da ake bukata ga Neymar a halin yanzu shi ne ya biya basussukan harajin da ake binsa kuma ba za a tura shi gidan yari ba.
Kotu ta kwace kadarorin Neymar
Wata kotu a Brazil ta bayar da umarnin a kwace kadarorin da shahararren dan kwallon FC Barcelona Neymar da Silba Santos Junior ya mallaka a…