✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kwace gwalagwalan sama da Naira biliyan 14 na tsohuwar Ministar mai

Da ranar yau Juma’a ne wata babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta kwace tarin kayan gwalagwale da suka hadar da daruruwan ‘yan…

Da ranar yau Juma’a ne wata babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta kwace tarin kayan gwalagwale da suka hadar da daruruwan ‘yan kunnaye da tsarkoki da awarwaro da wayar Ifone ta gwal mallakar tsohuwar Ministan mai ta Najeriya Diezani Alison Madueke.

Kayayyakin gwalagwalan wanda kotun ta kwace ta mallakawa Gwamnatin Tarayya an kiyasta kudin su akan Naira biliyan 14 da miliyan dari 4.

Hukumar yaki da ta’annati ga tattalin arzikin kasa ta EFCC ce ta gano kayan gwalagwalan a gidan tsohuwar Ministar wadanda ake ganin ta saye su ne ta hanyar da ba ta dace ba, da dukiyar kasa ko a baya ma kotu ta kwace kadarorin biliyoyin Naira na tsohuwar Ministar ta kuma mallakawa Gwamnatin Tarayya.