Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da wani dan cocin Seventh Day Adventist ya shigar yana neman a haramta gudanar da zabe a ranar Asabar a Najeriya.
A hukuncin da Mai shari’a James Omotosho ya yanke a ranar Laraba, ya bayyana karar a matsayin wani fada na rashin gaskiya, abin takaici da harzuka zuciya, kuma marar tushe.
Ya yi watsi da hujjar cewa gudanar da zabuka a ranar Asabar shiga hurumin ‘yancin mambobin cocin ne.
Wani dan cocin Seventh-day Adventist, Ugochukwu Uchenwa ne ya kawo karar, inda ya kalubalanci gudanar da zabe a Najeriya a ranar Asabar.
Ya ce wannan dabi’a ta zabe ranar Asabr take hakkinsu ne na ‘yancin yin ibada da kuma matsayinsu na ‘yan kasa da ake hana su shiga zabe.
- Shugaban ƙasar Vietnam Van Thuong ya yi murabus
- Tinubu Ya Roƙi ’Yan Majalisa Su Tsagaita Gayyatar Shugabannin Ma’aikatu
Alkalin ya jaddada cewa gwamnati na da hurumin tauye hakkokin duk wani dan kasa domin samun ci gaba, yana mai cewa a wannan batun ma ba a tauye hakkin cocin ba.
Ya kuma yi nuni da cewa cocin Seventh-day Adventist ‘yan tsiraru ne a Najeriya kuma ba za su iya dora koyarwar su a kan mafi yawan mabiya addinai a kasar ba.
A nasa banagaren, Benjamin Ahamaefule, lauya ga wanda ya shigar da karar, ya bayyana aniyarsa na kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke a kotun daukaka kara.