Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Babban Birnin Tarayya Abuja ta sauke Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, da Mataimakinsa, Eric Igwe, daga kujerunsu saboda komawa jam’iyyar APC.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, wanda ya yanke hukuncin ranar Talata ya ce sauya shekar ta su ta saba da Kundin Tsarin Mulki.
- ‘Mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu sun haura miliyan 2’
- ’Yan bindiga sun harbe ’yan sa-kai 63 a Kebbi
Kotun ta kuma umarci mambobin majalisar Jihar su 15 da su ma su sauka daga mukamansu saboda sauya shekar.
Kazalika, Kktun ta kuma umarci Gwamnan ya dawo da dukkan kudaden da ya karba a matsayin albashi da alawus-alawus tun bayan sauya shekar tasa ga lalitar Gwamnatin Jihar.
A ranar 17 ga watan Nuwamban 2020 ne dai Gwamnan ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP wacce aka zabe shi karkashinta, zuwa APC, bayan shafe tsawon lokaci a ana rade-radi a kan batun.
A lokacin dai, Gwamna Umahi ya ce ya sauya shekar ne don ya kawo karshen abin da ya kira rashin adalcin da ake nuna wa yankin Kudu masoi Gabas a PDP.
Tuni dai Gwamnan ya kuma bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a karkashin tutar jam’iyyar ta APC.