✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta karbi $61,400 matsayin shaidar Badakalar Abba Kyari

Kotu ta karbi kudaden a matsayin shaidar toshiyar bakin da DCP Abba Kyari ya bayar.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta karbi tsabar kudi Dala 61,400 da aka gabatar mata a matsayin shaida hancin da ake zargin dakataccen Kwamishinan ’Yan Sanda, Abba Kyari, ya bai wa jami’an Hukumar Yaki da Sha da Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya amince da hakan ne a zaman kotun na ranar Laraba bayan NDLEA ta gabatar masa da shaidarta ta hannun mai tuhuma na uku, Peter Joshua.

A ranar 22 ga Fabrairu aka gurfanar da DCP Abba Kyari tare da wasu abokan aikinsa, ACP Sunday Ubua da ASP Bawa James da Sufeto Simon Agirigba sai kuma Sufeto John Nuhu, sai kuma ASP John Umoru da ya tsere.

Yayin shari’ar, Joshua, wanda babban jami’in NDLEA ne a ofishin hukumar da ke Legas ya fada wa kotun cewa, a ranar 25 ga Janairu aka mika masa kudaden bayan ya kammala bincikensa a kan zaman kudin shaida.

NDLEA ta yi ikirarin tana da bidiyon yadda Abba Kyari yake tayin bayar da toshiyar bakin Dala 61,400 don hana yin gwajin wasu miyagun kwayoyi da da aka kama masu nauyin kilogram 17.55.

Kwayoyin wani bangare ne na hodar iblis mai nauyin kilogram 21.35 da aka kama an shigo da ita kasa ta Babban Filin Jirgi na Akanu Ibiam da ke Inugu, daga 19 zuwa 25 ga Janairu.

Kazalika, jami’in ya gabatar wa kotun kullin hodar ibilis da dama a matsayin karin hujjoji.

Daga bisani, alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ran 30 ga Agusta mai zuwa.