✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta hukunta Cardi B saboda dukan wasu mata a gidan rawa

Kotu ta yanke wa fitacciyar mawakiyar gambarar zamanin nan ta duniya, Belcalis Marlenis Almánzar, wacce aka fi sani da Cardi B, hukuncin hidimta wa kasa…

Kotu ta yanke wa fitacciyar mawakiyar gambarar zamanin nan ta duniya, Belcalis Marlenis Almánzar, wacce aka fi sani da Cardi B, hukuncin hidimta wa kasa na kwana 15.

Kotun ta yanke mata hukuncin ne bayan ta amsa laifin yi wa wasu mata biyu, Jade da Baddie Gi, duka a gidan rawar Angels a shekara 2018.

Laifukan da aka tuhumi Cardi B da wasu da suka taya ta dukan, sun hada da cin zarafi, da jefa rayuwa cikin hatsari da gangan.

Kazalika, kotun ta sarauniya ta kuma hana mawakiyar sanya kafa inda matan suke.

Tun da fari dai Cardi B ta sanya a yi wa matan duka, bisa zargin daya daga cikinsu da zama dadiron mijinta mai suna Offset.

“Alamun girma shi ne amsa laifinka, kuma a matsayina na uwa da ke son yarana su tashi da gaskiya, ya sa na nuna misali da kaina.

“A baya na yanke danyen hukunci kan abubuwa da yawa, wadanda ba na shakkar  fuskantar sakamakonsu a yanzu.

“Wadannan kura-kurai ba su ke nuna wacece Cardi B ta yanzu ba. Don haka na shirya girbar abin da na shuka,” inji ta.